SIHIRIN SAKAR WA MACE JINI

Menene sihirin sakar wa Mace Jini

Yadda suke kulla sihirin sake wa Mace Jini

Alamomin sihiri sakar wa Mace Jini

Matakan da ake bi domin warware sihirin sakar wa Mace

SIHIRIN SAKE WA MACE JINI:

Sihirin sake wa mace jini anfi yin shi ga Mata. A wajen Malaman Fiqihu suna kiranshi da jinin istihadha a wajen masu Magani kuma ana kiranshi da sihirin nazif. Idan aka yi wa mace wannan sihirin zai sa ta rinka ganin jini na zuwa mata a kowane lokaci, ba lalai sai a lokacin al’adanta ba. Idan ya kasance mace tana ganin jini na zuwa mata a ba lokacin al’adar da ta saba gani wata wata ba, kuma babu wani dalili na dabi’a. Misali an bincika ba ta da cutar sanyi mara (urinary track infections, pelvic immflamentory deseases), kuma bata samu matsalar barin ciki ba (wato babu lalacewar ciki)? Domin dukkan wadannan cututtukka da muka ambata suna iya haddasa wa mace ganin jini ba a lokacin al’adarta ba. A takaice sihirin sake wa mace jini kan haddasa mace ta rinka ganin jini haka kawai ba tare da wani dalili ba face na sihiri.

Yadda ake kulla Sihirin sake wa Mace jini

Wanda yake son a aikata masa wannan nau’i na sihiri yakan je wajen boka ko mai sihiri ya nemi ayi masa aikin sihiri akan matar da yake so a sake mata jini. Shi kuma mai sihirin zai tsayu da aikin sihirin wanda zai tura wa wannan matar aljanin da za a kallafawa gudanar da wannan sihiri bayan ya karbi wasu bayanai na ta da kuma kayan aikin hada sihirin. Aljanin zai shiga jijiyon jini na wannan matar wanda ya je har mahaifarta zai rinka gudu a ciki har ya sake mata jini. Annabi tsira da amincin Allahsu kara tabbata a gare da iyalan gidansa yana cewa:

يقول النبي صلى عليه وآله وسلم :

 «الشَّيطانُ يجري من ابن آدم مجرى الدم ) . فإذا وصل الجني إلى عرق معروف في الرَّحِم رَكَضَه ركضة فسالَ هذا العرق دما.يقول النبي عندما سألته حمنة بنت جحش عن الاستحاضة: «إنمـا هـي . رَكْضَةٌ من ركضات الشيطان»

Fassara:

“Shaidan ya na tafiya a jikin dan Adam a magudanar jini. Idan ya isa jijiyan da aka sani da jijiyar mahaifa zai ya yi sassarfa a wajen sai wannan jijiyar ya fitar da jini. Annabi (S) na cewa: A lokacin da Hamnatu binta Jahash ta tambaye shi dangane da istahala: ((Ya na kasanewa sassarfa daga sassafar shaidan)).

ALAMOMIN SIHIRIN SAKE WA MACE JINI:

Kafin kawo bayanin yadda za magance wannnan nau’in sihirin ya na da muhimmancin muka wasu daga cikin alamomin gane sihirin sake wa mace jini. Wadannan alamomi su suka fi aukuwa ga wadda aka yi wa sihirin sake wa mace jini:

1- Saukar jini daga farjin mace ba ta inda hailanta ke zuwa ba kuma babu wani cuta sananniya a wajen likitoci.

2- Za ta rinka jin zafi mai tsanani a inda mahaifanta yake.

3- Za ta rinka jin ciwon baya daga wajen konkwasonta.

4- Zata kasance bata son sauraren karatun Al-Kur’ani mai girma.

5- Zata rinka nisantar sallah da zikiri.
6- Mace za ta rinka gudun mijinta

7- Za ta rinka jin kamar ana shafan jikinta a cikin bacci/kwana ko a falke.

Yadda Za a Warware Sihirin Sake Mace Jini

Akwai matakai na magani da dama da ake amfani da su wajen lalata sihirin sake wa Mace jini ga wasu kadan daga ciki:

1- Ana karanta ayoyin rukiya a cikin ruwan mai tsafta da zarki a ba mara lafiyan ta sha ta yi wanka na tsawon kwana uku a jere. Ga ayoyin a kamar haka:

سورة الفاتحة

“بسم الله الرحمن الرحيم، الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِ الْعَالَمِينَ، الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ، مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ، إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ، صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِم، غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ”. 

آية الكرسي

“اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيم”. 

سورة الأعراف من الآية 117 حتى 121

“وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ، فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانْقَـلَبُوا صَاغِـرِينَ وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ، قَالُوا آَمَنَّا بِرَبِ الْعَالَمِينَ”. 

سورة يونس من الآية 79 حتى 82

“وَقَالَ فِرْعَوْنُ ائْتُونِي بِكُلِ سَاحِرٍ عَلِيمٍ، فَلَمَّا جَاءَ السَّحَرَةُ قَالَ لَهُمْ مُوسَى أَلْقُـوا مَا أَنْتُمْ مُلْقُونَ، فَلَمَّا أَلْقَوْا قَالَ مُوسَى مَا جِئْتُمْ بِهِ السِحْرُ إِنَّ اللَّهَ سَيُبْطِلُهُ إِنَّ اللَّهَ لا يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ، وَيُحِقُّ اللَّهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ”. 

سورة طه من الآية 65 إلى 69

“قَالُوا يَا مُوسَى إِمَّا أَنْ تُلْقِيَ وَإِمَّا أَنْ نَكُونَ أَوَّلَ مَنْ أَلْقَى، قَالَ بَلْ أَلْقُوا فَإِذَا حِبَالُهُمْ وَعِصِيُّهُمْ يُخَيَّلُ إِلَيْهِ مِنْ سِحْرِهِمْ أَنَّهَا تَسْعَى، فَأَوْجَسَ فِي نَفْسِهِ خِيفَةً مُوسَى، قُلْنَا لَا تَخَفْ إِنَّكَ أَنْتَ الْأَعْلَى، وَأَلْقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلْقَفْ مَا صَنَعُوا إِنَّمَا صَنَعُوا كَيْدُ سَاحِرٍ وَلَا يُفْلِحُ السَّاحِرُ حَيْثُ أَتَى”. 

سورة البقرة الآية 222

“وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّى يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ”.

سورة الفرقان الآية 23

“وَقَدِمْنَآ إِلَىَ مَا عَمِلُواْ مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَآءً مّنثُوراً”. 

 سورة الطلاق الآية 4

“وَاللَّاتي يَئِسْنَ مِنَ الْمَحِيضِ مِنْ نِسَائِكُمْ إِنِ ارْتَبْتُمْ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَاثَةُ أَشْهُرٍ وَاللَّائِي لَمْ يَحِضْنَ وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَنْ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مِنْ أَمْرِهِ يُسْرًا”.

سورة آل عمران الآية 6

“هُوَ الَّذِي يُصَوِّرُكُمْ فِي الْأَرْحَامِ كَيْفَ يَشَاءُ لا إِلَهَ إِلا هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ”. 

سورة لقمان الآية 34

“إِنَّ اللَّهَ عِنْدَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ الْغَيْثَ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْأَرْحَامِ وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ مَاذَا تَكْسِبُ غَدًا وَمَا تَدْرِي نَفْسٌ بِأَيِّ أَرْضٍ تَمُوتُ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ”. 

سورة الإخلاص

“قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَد ، اللَّهُ الصَّمَدُ، لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ”. 

سورة الفلق

“قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ، مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، وَمِنْ شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ، وَمِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ، وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ”. 

سورة الناس

“قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ، مَلِكِ النَّاسِ، إِلَهِ النَّاسِ، مِنْ شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ، الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ، مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ”. 

 من سورة الأنعام الآية 13

“وله ما سكن في الليل والنهار وهو السميع العليم”.

Mataki na biyu:

Ana hada tawadar turaren miski da garin Za’afaran da ruwan wardi a umurci wata mace daga makusantar mara lafiyar ta rubuta wannan ayar da surorin da za mu kawo a kasa, a farar takarda mara rubutu. Bayan an rubuta za a nade, ta daura a kasan cibiyarta idan jini ya dauke sai ta cire. Ga ayar da surorin da ake rubutawa:

“قيل يا أرض ابلعي ماءك ويا سماء أقلعي وغيض الماء وقضي الأمر”

سورة الفاتح

آية الكرسي

سورة الكافرون

سورة الإخلاص

سورة الفلق

سورة الناس

Mataki na uku:

A nemi garin habbatus-sauda cokali 10, garin hulba cokali goma, tafarnuwa cokali 5, garin sazabu cokali biyar da garin yansun cokali biyar a hada wuri guda a yamutsa sosai sai rinka diban cokali guda ana sanya wa cikin ruwan zafi karamin kofi bayan miti 7 a tace a sanya zuma a sha. Za rinka sha da safe da yamma.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *