- Menene Sihirin rashin lafiya
- Alamomin dake gane rashin lafiya na sihiri
- Maganinin Sihirin rashin lafiya
SIHIRIN RASHIN LAFIYA
Sihirin rashin lafiya wani nau’in sihiri ne wanda manufar wanda yayi wannan sihirin shi ne ya sa wanda aka yi wa sihirin ya kamu da rashin lafiya. Zai rinka jin ciwo da radadi a jikinsa, kuma yanayin jikinsa zai sauya daga karfi jiki da nishadi zuwa raunin jiki da rashin kuzari.Har wayau sihirin rashin lafiya na iya kama kowace gaba daga cikin gabban mutum kuma zai iya masa tasihiri a wajen tunaninsa da kuma iya kiyaye abubuwan da ke kusa da shi.Sihirin rashin lafiya na iya kasancewa jifa ko sammu. Yana iya rike wa mutum hannu ko kafa ko kuma ya sanya mutum makanta ko shanyenwar bangaren jiki. Bugu da kari, sihirin rashin lafiya na iya ciraita daga wani gaba zuwa wani gaba na jikin dan Adam. Saudayawa idan likitocin zamani sun yi gwagwaje ba za su ga kowane ciwo ba. Alhali shi wanda aka yi wa sihirin yana jin tsananin ciwo a jikinsa. Kuma misali likitoci na iya yin gwaje gwaje a yau a samu yana da wani ciwo amma idan aka koma gobe a ga babu wannan ciwon duk kuwa da kasancewa bai sha kowane magani ba.
Yana iya yiwuwa mai sihiri ya aika wa mutum daya daga cikin al’ajanu sai mutumin ya kamu da rashin lafiya,idan da wannan da aka yi masa sihirin zai je wajen likitoci su rubuta masa magani to ko ya sha ba zai ji wani sauyi ba kuma ba zai warke daga wannan rashin lafiyar ba.
Yadda ake haddasa sihirin rashin lafiya:
Me sihiri ko Boka yakan nemi taimakon aljani da shaidanu sai ya tura daya daga cikinsu zuwa ga mutumin da ake so ayi wa sihirin domin ya tsaya a wani wuri cikin jikinsa ko ya rike wani gaba daga jikinsa yana iya sanya wannan gaba ya shanye ko ya rike hawasa na shi tayiwu ya haddasa masa makanta ko kurumta da sauransu.
ALAMOMIN SIHIRIN RASHIN LAFIYA
Akwai alamomin masu yawa wanda ka iya faruwa ga wanda aka yi wa sihirin rashin lafiya. A wannan takaitaccen rubutun zamu kawo kadan daga ciki wanda suka hada da:
1- Akwai alamar sihirin rashin lafiya da ke shafar hankalin mutum wanda ke haifar shanyewa daya daga cikin gabban jikin mutum ko gaba daya jikin nasa.
2- Sihirin rashin lafiya wanda ke haddasa matsolin a cikin tsarin narkewar abinci kamar ya rinka haddasa masa ciwon ciki da amai da gudawa.
3- Akwai nau’in sihirin rashin lafiya dake haifar da matsalar numfashi kamar rikewar numfashi.
4- Daga cikin alamomin sihirin rashin lafiya akwai wanda ke haddasa ciwon gabobi, ciwon baya da na kashi ko kuma samuwar matsala a lakka.
Wani lokaci sihirin rashin lafiya baya takaituwa da wadannan alamomin da muka kawo,yakan haifar da jin tsoro a kodayaushe, da yawan kuka, mutum ya rinka son ya zauna shi kadai da miyagun mafalkai ko kuma yawan samun hare-hare a cikin bacci.
Tambihi: A lura faruwan wadannan alamomin da muka ambata ba sa wadatarwa a hukunta cewa da zaran an ji su shi kenan mutum an yi masa sihirin rashin lafiya. Akwai bukatar a tuntubi kwararru tare da bincike mai zurfi kafin daukan matsaya musamman akan abubuwa masu muhimmanci irin abin da ya shafi lafiya.
MAGANIN SIHIRIN RASHIN LAFIYA:
Akwai hanyoyi da dama wadanda likitocin musulunci su ka yi bayani wanda za a yi bin su wajen lalata sihirin rashin lafiya tare da samun waraka da yardan Allah Madaukakin Sarki. Daga ciki akwa dannan hanyoyi da za mu kawo kamar haka:
1- Yana muhimmacin wanda aka yi wannan nau’i na sihiri ya daga da aikata ayyukan alheri da zai samu kusanci da Allah Mai girma da Daukaka. Ya kuma nisanci sabon Allah iya iyawarsa. Wanda aka yi wa sihirin rabuwa ya daga da karatun Al-Kur’ani da addu’o’in neman waraka a wajen Allah domin a gurinSa ne kadai waraka take.
2- Wanda aka yi wa sihirin rabuwa ya nemi ma’aul-Wardi (Rose Water) ya tofa ayoyin rukiyya (mun kawo su a baya) a cikin wannan ruwan na wardi ya rinka sha da shafawa a jiki. Sannan ya rinka yayyafawa a gida da dakin da yake kwana.
3- wanda ke fama da sihirin rashin lafiya rinka sanya karatun surutul Bakara kullum yana sau rara a kalla sau uku a yini. Karatun Suratul Bakara na korar miyagul aljanu tare janyo alkhairai da arzaki a cikin gida.
4- Ya nemi man habbatus-sauda ya karanta ayoyin shifa a ciki ya rinka shafe dukkan ilahirin jikinsa sau uku a yina. Ayoyin shifa su ne wadannan ayoyi da za mu kawo kamar haka:
1. Suratul- Fatiha
2- Suratul Falaq da Suratun-Nasi
3- Wanunazzilu minal Kur’ani ma huwa shifa’un warahmatal-Limu’uminina.
4- (Bismillahi urqika, wallahu yashfika min kulli da’in yu’uzika, wa min kulli nafsi au ainin hasidin Allahu yasgfiika).
5- Allahumma Rabbin-Nasi Azhibba’asa washfi anta shafi la shafa’u illa shifa’uka shifa’un la yugadiru sakaman.
Ga sunan kamar yadda suke a larabci:
وهذه الرقية هي:
الفاتحة. -1
٢– المعوذات .
وَنُنَزِّلُ مِنَ الْقُرآن ما هو شفاء ورحمة للمؤمنين )
٤– (بسم الله أرقيك، والله يشفيك من كل داء يُؤذيك، ومِنْ كُلِّ نَفْسٍ أَو عَينِ حاسد الله يشفيك).
ه- (اللهم رب الناس، أذهب البأس، واشف أنت الشافي لا شفاء إلا شفاؤك شفاء لا يغادر سقما ) .