Ana kiran wannan nau’in sihirin ne da sihirin kira ko kuma wasu suce kiranye saboda shi wanda aka yi wa sihirin zai rinka jin ana kiranshi ba tare da ya ga mai kiransa ba, ko ya san daga inda kiran fitowa ba, sannan yana iya jin ana taba shi ko ana buga masa wani abu a kai ba tare da ya ga kowa ba. Har ila yau wannan sihirin na sa wa mutum waswasi da gusar masa da hankali wani lokaci wannan nau’in sihirin na tunkuda wanda aka yi wa zuwa ga ya kashe kansa.
Yadda ake sihirin Kira (Sihirul-Hawatif):
Yadda ake yin wannan nau’in sihirin shi ne Boka ko mai Sihiri zai aika aljani ko aljanu tare da kallafa masu cutar da mutumin da aka yi wannan sihirin yana cikin bacci ko a falke. Idan ya na bacci aljanin zai zo masa a siffan dabbabo da za su rinka binsa da kuma za a rinka kiranshi idan yana falke wani lokacin da muryar mutanen da ya sani, ko kuma bakin muryoyi. Sannan zai rinka kokonton shin wadannan sautin daga nisa ne ku kusa.
Alamomin wannan sihirin suna bambanta kuma ya danganta karfin sihirin ko rashin karfinsa.
ALAMOMIN SIHIRIN KIRA:
Akwai alamomi da yawa da ake gane nau’in sihirin kara wanda ya kamata mu sansu daga cikin wadannan alamomi sun hada da:
1- Wanda aka yi wannan nau’in sihiri zai rinka yin mafalkai masu ban tsoro misali zai rika yin mafalki an kawo masa hari (attack) wanda hakan zai sanya ya falka daga baccin kuma zai ji tsoron sake komawa bacci.
2- Bayan harin da zai rinka fuskanta a cikin mafalki har wayau zai rinka mafalkai da dabbobi wadanda suke baki wadanda bai taba ganinsu ba kamar dai yadda zai rinka mafalkai da karnuka da kuma macizai.
3- Zai rinka yin mafalkin ya na kan wani tudu,
bene mai tsayi ko wani wuri kololuwa ko yana cikin rijiya hakan zai sanya ya rinka jin tsoro a cikin mafalki kuma haka nan zai ci gaba da jin tsoron bayan ya falka.
4- Zai kasance mai yawan waswasi a kowane lokaci.
5- Zai rinka fama da ciwon baya musamman daga kasan bayanshi.
6- Yawan fitsari
7- Yawan ciwon kai da saukan jini
8- Zai rinka mafalki ana kiranshi.
Yadda Ake Warware Sihirin Kira:
Anan warware wannan nau’in sihirin ta wadannan hanyoyi da za mu kawo da yardan Allah.
Mataki na farko:
1- Ana karanta wa mutumin da ke fama da sihirin kira ayoyin rukiya idan aljanin ya yi maganan zai a nemi sanin inda sihirin yake a warware ko a nemi ya fita ya bar jikin mara lafiya idan kuma bai yi magana ba to ayi amfani da wadannan hanyoyi kamar haka:
Mataki na biyu:
(a) Mara lafiya rinka yin alwala kafin ya kwanta bacci kuma rinka karanta ayatul-kursiyyu
(b) Ya rinka hada tafin hannuwanshi yana karanta suratul-falaq da suratul Nasi yana tofawa ya shafa jiki sau uku kafin ya kwanta bacci.
(c) Ya rinka karanta suratul Safat da suratul-Dukhan ko kuma ya saurarin karatun wadannan surori safe da kuma lokacin da zai kwanta bacci. http://www.alwahada.com.ng
(d) Karatun Suratul-Bakara duk bayan kwana uku ko kuma sauraren sautin karatun.
(e) Zikirin “ Hasbiyallahu la’ilaha illahuwa alaihi tawakaltu wa huwa rabbul-arshil azim. Kafa bakwai.
(f) A sajjala (recording) wadannan surori ya na saurara da safe da yamma: Suratul-Fussilat, Fathi, da suratul Jin ya rinka saurara sau uku a kowani rana.