SIHIRIN HANA SADUWA A TSAKANIN MATA DA MIJI:

Sihirin hana namiji saduwa da matarsa ko hana mata ta yadda da mijinta a lokacin da ya zo saduwa da jima’i da ita. Wannan wani nau’in sihiri ne da ake yi domin a hana azzakarin namiji ya mike a lokacin da ya zo saduwa da matarsa duk kuwa da cewa lafiyarsa kalau a bangaren mazakuta. Wannan sihirin su ma mata akan yi masu shi ta yadda idan namiji ya zo saduwa da su sai gabansu ya toshe, ko ta hana mijinta ya shigeta kuma ta na yin hakan ne ba a cikin hayyacinta ba, ko kuma da zarar mijinta ya zo saduwa sai jini ya zo mata, ko kuma ya kasance ba ta jin dadin saduwar kwata-kwata a dalilin wannan sihirin da aka yi mata.

Yadda Ake Haddasa Sihirin Hana Saduwa:

Shaidanin aljanin da aka wakilta da wannan nau’in sihirin yakan je ya zauna a kwakwalwar namiji, ya kan tsaya a daidai gabar da ke aika sakonnin sha’awa a lokacin jima’i. Wannan aljanin yakan bar sassan gabobin jima’i su yi ayyukansu na dabi’a (azzakarinshi zai rinka ta shi kuma zai rinka jin sha’awa) amma da zaran ya kusanci matarsa yana so ya sadu da ita daga nan wannan Shaidanin aljanin ya yanke hanyoyin sadarwan sha’awa daga kwakwalwarsa wanda zai hana jinin da ke tafiya cikin gaggawa dake sanya azzakarin namiji ya mike, sai ya hana jinin isa ga mazakutarsa hakan zai sanya azzakarin ya kwanta ko da kuwa a baya azzakarin na sa yana a mike.

Shi yasa wani lokacin za ka ga wanda aka yi wannan sihirin azzakarinsa kan mike sosai idan yana wasa da matar amma da zaran ya zo saduwa da ita sai azzakarin ya kwanta.

Wani lokaci idan namiji na da mata biyu ko fiye da haka yana iya kasancewa idan ya zo wajen daya daga cikin matan zai sadu da ita lafiya kalau amma da zaran ya je ga wanda aka yi masa sihiri a kanta to ba zai iya saduwa da ita ba.

ALAMOMIN SIHIRIN HANA SADUWA:

1- Ciwon kai akai akai kuma koda an sha magani ba za a warke ba.

2 Yawan Jin kunci a kirgi musamman daga bayan la’asar zuwa rabin dare.

3- Rashin mikewar azzakari a lokacin da mutum ya zo saduwa da matarsa.

Hanyoyin Warware Sihirin Hana Saduwa:

Daga cikin hanyoyin da ake amfanin da su wajen warware wannan sihirin sun hada wadannan da za mu kawo kamar haka:

1- Akan karanta wa wanda aka yi wannan sihirin ayoyin rukiya wanda muka kawo a baya, idan aljanin da aka wakilta da wannan sihirin ya yi magana sai a tambaye shi inda aka ajiye sihirin sai cire shi a lalata. Daga nan a nemi aljanin ya fita daga jikin mara lafiya idan ya fita shi ke nan sihirin ya lalace. Amma idan bayan an yi rukiya aljanin bai yi magana ba sai a bi wasu daga cikin hanyoyin magani.

2- Ana karanta wadannan ayoyi da za mu kawo a kasa cikin ruwa tsarkakke a sha ayi wanka da wannan ruwan na tsawon kwana bakwai sihirin zai lalace da iznin Allah. Ga ayoyin kamar haka:

﴿قَالَ مُوسَى ما جِئْتُم  بِهِ السِّحْرُ إِنَّ اللهَ سَيُبْطِلُهُ إِنَّ الله لا يصلح عمل الْمُفْسِدِينَ وَيُحِقُّ اللهُ الْحَقِّ بكلماته وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ. وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِي تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ . فوقع الْحَقِّ وبطل ما كَانُوا يَعْمَلُونَ . فَعَلُبُوا هنالك وانقلبوا صاغرين . وألقي السحرة ساجدين . قَالُوا آمنا برَبِّ الْعَالَمِينَ. رَبِّ مُوسَى وَهَارُونَ . إِنَّمَا صَنَعُوا كَيْدُ ساحِرٍ وَلَا يُفْلِحُ الساحر حيث أتى .

3- A samu gayen magarya danye a samu duwatsu guda biyu daya a dora ganyen magaryan akansa daya kuma ayi amfani da shi wajen dandaka ganyen magaryan sai sanya a cikin kwanon da aka zuba ruwa a cikin sai kusanto da kwanon kusa da baki a karanta wadannan ayoyi:

1- Ayatul-Kursiyu kafa 7, suratul falaq 7, suratun-Nasi 7, sai ayi ta shan wannan ruwan ana wanka da shi tsawon kwana bakwai ba za a kara wani ruwa ba, kuma ba za a dafa ba idan ta kama sai an duma saboda sanyi to a sanya ruwa cikin rana. Idan aka yi haka da izinin Allah sihirin zai baci.

4- A karanta wannan aya da zamu kawo a kasa a cikin kunnen Wanda aka yi wa sihirin hana saduwa kafa dari (100):

وَقَدِمۡنَآ إِلَىٰ مَا عَمِلُواْ مِنۡ عَمَلٖ فَجَعَلۡنَٰهُ هَبَآءٗ مَّنثُورًا

5- A nemi garin sazabu a rinka diban babba cokali ana sanyawa cikin ruwan zafi a rinka wanka da shi na tsawon sati biyu (14) kuma har wayau a rinka hayaki da hayakin shaidanu sau biyu a rana.http://www.alwahada.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *