SIHIRIN DA YA HALASTA

A wannan takaitaccen rubutun zamu kawo bayani dangane da sihiri na halas a mahangar Malamai:

Kasancewar mun kawo hujjojin tabbatu da ke nuni da cewa zuwa wajen Boka da kuma yin sihiri haramun ne a Musulunci kuma yana iya jefa mai aikatawa zuwa ga halaka na har abada. To akwai bukatar Mace Mumina ta sani cewa akwai nau’in sihiri da za ta iya yi ta samu soyayyar mijinta tare da samun cikakken kulawa daga gare shi. Kuma aikata irin wannan sihiri da irin wannnan ma’anar da zamu kawo ba haramun ba ne.

Mace na iya sihirce majinta da abin da Allah ya halatta mata ta hanyar yawan yi masa ado, sanya turare ta yadda ba zai ji wani wari daga gare ta ba,kulawa da tsafta jiki da muhalli,yawan yi masa murmushi da kyawawan kalamai. Ta kasance wanda ta iya mu’amala tare da kiyayewa da kula da dukiyar miji. Kyautatawa da kulawa da ya’yan Mijinta, yi masa biyayya sau da kafa sai dai akan abin da yake sabon Allah ne. Ba a biyayya ga abin Halitta a wajen saba wa Mahalicci. Har ila yau tana iya karawa da addu’o’in da suka halitta akan Allah ya ba su zaman lafiya da kaunar juna ya kuma kare su daga sharrin mutum da aljani.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *