SHAWARWARI AKAN YADDA ZA A WARWARE SIHIRI

Idan muka lura da kasancewar sihiri cuta ce da take samun jiki, ta sanya mutum rashin lafiya wanda hakan zai sa wasu abubuwa su rinka faruwa da shi tare cutar da tunaninsa. Dan haka yana da muhimmmanci mutum ya yi kokari iya iwarsa wajen neman magani ta hanyar da ta halitta domin samun lafiya. Ga wasu daga cikin hanyoyi da ake bi wajen warware sihiri:

1- Lalata Sihiri da Sihiri: Idan mutum yana da iko kuma ya san yadda ake sihiri da kuma bata shi, wanda idan har lalata sihirin zai kai shi ga aikata miyagun laifuka, aikata haramun ko shirka da Allah to wajibi ne ya nisanci yin hakan.Ke nan baya halitta bata sihiri da sihiri ko abin da ya ke haramun. Ga dai hadisin da aka ruwaito daga Manzon Allah kamar haka:

جاء عن الرسول -صلّى الله عليه وسلّم- في صحيح البخاري: (اجتنبوا السبع الموبقاتِ، قالوا: يا رسولَ اللهِ، وما هنّ؟ قال: الشركُ باللهِ، والسحرُ، وقتلُ النفسِ التي حرّم اللهُ إلّا بالحقِّ، وأكلُ الربا، وأكلُ مالِ اليتيمِ، والتولي يومَ الزحفِ، وقذفُ المحصناتِ المؤمناتِ الغافلاتِ)

Ya zo daga Manzo Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da Iyalan gidansa. – A cikin Sahihul-Bukhari (Ku nisanci abubuwa guda bakwai masu halakarwa, Su ka ce ya Ma’aikin Allah wadanne laifuka ne? Sai ya ce: Shirka da Allah, yin sihiri, Kisan rai wanda Allah ya haramta sai dai akan gaskiya, cin riba, cin dukiyar marayu, juya baya a wajen yaki, da yi wa mace katangaggiya kazafi (Jifar matan aure da zina).

2- Ana warware sihiri ta hanyar amfani da ganyen magarya. Yadda ake yi kuwa shi ne za a samun danyen ganyen magarya guda bakwai sai a samu duwatsu guda biyu daya a dora ganye akai daya kuma ayi amfani da shi wajen dandaka ganyen. Sai a sanya ganyen magaryar nan da aka dandaka cikin kwano ko kwarya a zuba sannan a sanya ruwan dumi da gishiri dan kadan ciki sai a karanta ayoyin rukiya a ciki ayi wanka. Ayi ta maimaitawa na tawawon kwana goma sha hudu. In sha Allah za mu kawo ayoyin rukiya nan gaba.

3- Ana Lalata sihiri ta hanyar yawan karatun Al-Kur’ani mai girma da sauraren ayoyin rukuya da kuma karanta wadannan surorin: Suratul-Falaq, Suratul Nasi, Suratul-IkhlasSuratul Kafirun, ayatul kursiyyu da Karatun Amana Rasul. Yawan karanta wadannan surori da niyyar lalata sihiri kuma dole ya kasance ana da alwala su na taimakawa sosai sannan suna da matukar tasiri wajen bata sihiri.

4- Cin dabino ajwa: Yana daga cikin hanyoyi da ake bi waje bata sihiri cin dabinon ajwa. Akwai hadisai da yawa da aka ruwaito wanda ke nuni da cewa cin dabinon ajwa na lalata sihiri. Ga daya daga cikin hadisan kamar haka:

وردت العديد من أحاديث الرسول -صلّى الله عليه وسلّم- في فضل التمر في علاج السحر منها: (من تصبَّحَ كلَّ يومٍ سبعَ تمَراتٍ عجوةً، لم يضرَّه في ذلك اليومِ سمٌّ ولا سحرٌ)

Wanda ya wayi gari yana cin dabinon ajwa guda bakwai a kowace rana sammu ko sihiri ba zai cutar da shi a wannan ranar ba’’.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *