- Ma’anar Sihirin Rabuwa
- Yadda ake kulla Sihirin Rabuwa
- Alamomin Sihirin Rabuwa
- Yadda ake Maganin Sihirin Rabuwa
SIHIRIN RABUWA
Sihirin rabuwa shi ne nau’in sihirin da ake yi domin raba mata da miji tare da Sanya kiyayya a tsakaninsu ko ya sanya kiyayya mai tsananin a tsakanin abokai biyu. Ire-ren wannan sihiri sun hada sihirin raba mata da miji,sihirin raba Uwa da Danta,sihirin raba Uba da Dansa, sihirin raba yaya da kani, sihirin raba mutun da abokinsa da kuma sihiri raba dan kasuwa da abokan kasuwancinsa (A raba mutum da masu sayayya a wajensa).
Sihirin rabuwa na daya daga cikin nau’in sihirin da ya zo a cikin Al-Kur’ani mai girma kamar yadda yake a cikin wannan ayar da za mu kawo kamar haka:
وَاتَّبَعُوا مَا تَتْلُو الشَّيَاطِينُ عَلَىٰ مُلْكِ سُلَيْمَانَ ۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَٰكِنَّ الشَّيَاطِينَ كَفَرُوا يُعَلِّمُونَ النَّاسَ السِّحْرَ وَمَا أُنْزِلَ عَلَى الْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَارُوتَ وَمَارُوتَ ۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ ۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَيْنَ الْمَرْءِ وَزَوْجِهِ ۚ
Fassara:
“ Kuma sun bi abin da shaiɗanu ke bi don karya mulkin Sulaiman. Sulaiman bai kafirta ba, amma Shaiɗanu ne suka kafirta. Sona koya wa mutane sihiri. Kuma suna riya bin abin da aka saukar wa Mala’iku biyu, a Babila – Haruta da Maruta. Su kuwa ba sa koya wa kowa komai, sai sun ce. Haƙiƙa, mu fitina ne, kada ka kafirta. Daga gurinsu su ke koyon abin da suke amfani da shi, suke rarraba tsakanin mutum da matarsa….”
YADDA AKE KULLA SIHIRIN RABUWA
Mutumin da ke neman ayi masa irin wannan nau’in sihirin yakan je wajen Boka/Mai Sihiri ya ce masa yana son a raba wani da matarsa ko wani da abokansa daga wannnan mai sihirin zai nemi sunayen wadanda yake so a raba. Wani lokaci su kan nemi gashi ko riga ko hular wadanda za ayi sihirin a kansu. Idan aka kawo masa abin da ya nema sai ya fara aikin sihirin wani idan ya hada sihirin zai bayar a sanya a bola,masai ko wajen kazanta ko kuma inda wadannan masoyan ko ma’aurantan ke wucewa.
ALAMOMIN SIHIRIN RABUWA
1- Yana daga cikin alamomin sihirin rabuwa canzawa hali a lokacin kankani daga soyayya zuwa kiyayya.
2- Girmama dalilan sabani ana iya rabuwa akan dalili kankani.
3- Rashin kabar uzurin juna, duk wani uzuri da zaka bayar ba zai karba ba.
4- Canzawa surar namiji a idon matarsa da kuma canzawar surar Mace a idon Mijinta. Namiji zai rinka ganin matarsa da mummunar kama koda kuwa matar ta sa tana cikin kyayawan mata, haka mata za ta rinka ganin majinta da mummunan kama. Abin da yake hakika shi ne shaidanin da aka wakilta da wannan sihirin ne ke sauya masu kama zuwa mummuna.
5- Yawan kokonto a tsakaninsu
6- Rashin son zama waje guda da wanda aka yi wa sihirin
7. Wani lokaci idan Miji na waje zai kasance cikin hali mai kyau yana fara’a da farin ciki amma da ya shigo gida sai ya rinka jin kunci da bacin rai mai tsananin a ransa.
Yadda ake Maganin Sihirin rabuwa
Daga cikin hanyayin warware wannan nau’in akwai komawa zuwa ga Allah ta hanyar tuba da Istigfari da zurfafawa da addu’a tare da Kankan da kai wajenSa tare da sanin cewa wajen Allah maganin yake kuma babu abin da zai samu mutum sai abin da Allah ya rubuta masa. Wanda aka yi wannan nau’in sihirin na iya karanta wannan addu’ar da zamu kawo a kasa:
«اللهم إنك أقدرت بعض عبادك على السحر والشر، ولكنك احتفظت لذاتك بإذن الضر، فأعوذ بما احتفظت به مما أقدرت عليه بحق قولك الكريم: «وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِنْ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ
2- (a) Matakin na biyu na warware sihirin rabuwa; wanda yake fama da wannan nau’in sihirin ya rinka saurare sautin karatun suratul Yasin, suratul Dukhan da suratul Jin sau uku a rana da sharadin ya kasance da al’awala kuma ya yi niyyar sauraron karatun da nufin neman waraka a wajen Allah Ta’ala.
(b) Yawan istigfari a kalla ya yi istigfari sau dari kullum ko fiye da haka.
(c) Yawan zikirin “La haula wala kuwwata illa billa” sau dari kullum ko fiye da haka.
Matakin na uku: Ana iya amfanin da magungunan karya sihiri da korar miyagun aljanu daga jikin dan Adam. Daga cikin maganin da za mu bayar da shawara ayi amfanin da shi shi ne: A nemi man habbatus-sauda kwalba guda, man tafarnuwa rabin kwalba da man gelu rabin kwalba a hada wuri guda a tofa suratul fatiha, Ikhlas, falaq da Nasi da ayatul kur’siyyu a ciki.A rinka shafawa da safe da yamma sihirin zai lalace da yardan Allah.