Menene Sihiri ?

SIHIRI

Kalmar sihiri ta samo asali ne daga yaren larabci wanda Malaman Lugga suka yi bayaninta kamar haka:

Laisu ya ce: Sihiri aiki ne da ake neman kusanci da shi zuwa Shaidan da neman taimakonsa.

Azzahari ya ce: Asalin sihiri shi ne juyar da wani abu daga hakikaninsa zuwa ga wani abun daban.

Ibn Manzur ya ce: Kai kace mai sihiri ya yin da ya ga banna a cikin sura ta gaskiya sai ya yi rufa idon wannan abun zuwa ga hakikaninsa, hakika ya juya wannan abun zuwa wani abu.

Kalmar Sihiri a Istilahi:

Malam Fakharu Din Arrazi ya ce: Sihiri a shari’a ana saninsa da cewa; Ya kebanci duk wani abu da dalilin aukuwansa da jujjuyawansa zuwa abin da ba shi ne hakikansa ba, wannan abun zai rinka gudana a cikin sirri tare da yaudara.

Akwai ittifaki a tsakanin mai Sihiri da Shaidan akan cewa dole mai Sihiri zai rinka aikata wasu ayyuka da aka haramta da kuma ayyukan na tarayya da Allah (Shirka), a domin samun taimakon shaidan da yi masa biyayya cikin abin da ya nema daga gare shi.

Wasu daga cikin hanyoyin da Masu Sihiri suke samun kusanci zuwa ga Shaidan:

Wasu daga cikin masu sihiri sunka rubuta ayoyin Al-Kur’ani mai girma da najasa, sukan hada ayoyin kur’ani da jinin haila ko su rinka taka ayoyin kur’ani da wulankatasu. Wa su kan jefa ayoyin Kur’ani cikin Masai ko cikin kashi wasu suka bar wata sallar farilla ko kuma sun rinka sallah babu alwala. Wasu bokayen ka rinka yanka jarirai ko Zina da matan aure ko kananan yara. Wasu kan yi wa Matan aure rubutu a farji ko su yi masu wanka. Wasu kan yi Yasin tsirara ko su je gidin bishiya su yi sujjada da yanka wa shaidan ko wani al’ajani. Hanyoyin na saba wa Allah suna nan da yawa da masu sihiri suke aikatawa a dan haka yana da muhimmanci mu sani da Shaidan da mai sihiri abokan juna ne waje saba wa Allah Ta’ala.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *