A cikin wannan rubutu mun yi takaitaccen bayani dangane da hukunci Sihiri a Musulunci.
Haramun ne ga kowani Musulmi ya yi sihiri ko ya sa ayi masa. Wani abu da ya kamata mu sani shi ne duk lokacin da mai sihiri zai kulla sihirinsa sai ya aikata wani aiki na haram ko kuma aikata aikin da zai fitar da shi daga Musulunci. Idan muka lura tare da tadabburi da ayoyi da Hadisan da suka gabata za su kara tabbatar mana da haramcin sihiri da Bokanci. Bugu da kari, wannan hadisin da zamu kawo a kasa shi ma yana kara tabbatar mana da haramcin sihiri da zuwa wajen duba da kuma wajibcin nisantarsa. Ga hadisin kamar haka:
منها قول الرسول صلّى الله عليه وسلّم: (من أتى عرَّافاً فسألَه عن شيٍء لم تُقْبَلْ لهُ صلاةٌ أربعين ليلةً)،[١٣]
وعن عائشة -رضي الله عنها- قالت: (سألَ أُناسٌ رسولَ اللهِ -صلَّى اللهُ عليه وسلَّم- عن الكُهَّانِ، فقال لهم رسولُ اللهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم: لَيْسُوا بِشَيْءٍ، قالوا: يا رسولَ اللهِ، فإنَّهُم يُحَدِّثونَ أحْياناً بالشَّيءِ يكونُ حَقّاً؟ فقال رسولُ اللهِ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم: تِلكَ الكلِمَةُ مِنَ الحقِّ، يَخطَفُها الجنِّيُّ، فيَقُرُّها في أُذُنِ وليِّهِ قَرَّ الدَّجاجَةِ، فيَخْلِطونَ فيها أكثَرَ مِن مِائةِ كَذبَةٍ).
FASSARA:
Daga ciki akwai zancen Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da iyalan gidansa: “Wanda ya je wajen Boka ya tabbaye shi dangane da wani abu, ba za a karbi sallarsa ba kwana ar’aba’in”. An ruwaito haddisi daga Nana Aisha (R.A) ta ce: Wasu Mutane sun tambayi Manzon Allah (s.a.a.w) dangane da Bokaye sai Annabi “ Ya ce su ba kowa ba ne,sai suka ce ya Ma’aikin Allah (S), Su Bokayen wani lokacin su kan yi wasu zantuka wanda ya ke gaskiya ne, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya ce wannan maganar ta gaskiya aljani ke fada masu, sai ya jiyar da shi a kunnen wanda ya jibance shi irin jiyawar zakara sai ya rinka fada,a cikin maganganun akwai karairayi sama da dari”.