ALAMOMIN DA MUTUM ZAI GANE CEWA AN YI MASA SIHIRI.

A yanayin rayuwa al’umma a yau,akwai matsaloli da dama da suka shafi lafiyarsu,tattalin arzakinsu,matsalolin da suka shafi zamantakewa,matsalolin da ake samu a wajen aiki da wuraren sana’a. A gaskiya ba kowace matsala ba ce da ta shafi rashin samun kudade shiga, bangaren kasuwanci ko kuma bangaren lafiya za a iya ta’alakantashi da sihiri ba. Wasu abubuwan da ke faruwa akwai bukatar ayi nazari akan su ta hanyar amfani da hankalin da Allah ya yi mana wajen warwaresu. Wasu abubuwan kan faru saboda sakaci da rashin kulawa,wasu saboda lalaci da ranganci ko rashin tashin mu tsaye akan dugaduginmu kamar yadda hakan kan faru da wasun mu. Amma duk wadannan bayanai ba yana kore samuwan tasirin sihiri, hassada maita da sauransu ba ne. A’a ko kadan akwai su kuma suna faruwa a cikin al’ummah. Ga wasu daga cikin alamomin da ake gane cewa ayi wa mutum sihiri:

1- Bijire wa ibada gaba daya (wato zai kasance baya son yin ibada kwata-kwata) da kuma kauracewa ambaton Allah,rashin son sauraran wa’aziya da rashin son sauraron karatun Al-Kur’ani Mai tsarki.

2- Yawan yin mafalkai masu firgitarwa sannan za a rinka yin mafarkin an kawo masa hari a cikin baccinsa.

3- Daga cikin alamar sihiri a jiki akwai yawan ciwon kai a koda yaushe kuma ko an sha magani baya bari. Ko kuma canzawar fatan jikin mutum musamman fuskarsa.

4- Mutum ya rinka jin kamar yana tashi sama ko ana kora shi, yawan jin rauni da rashin tsayawa waje guda da kuma saurin rudewa da mantuwa.

5- Juyawan idanuwa da karkacewarsa

6- Har wayau, mutumin da aka yi wa sihiri zai rinka ganin wasu abubuwa ko kuma ya rinka jin kamar abu ya faru al’hali bai faru ba a hakika.

7- Daga cikin alamomin sihiri akwai yawan fushi da bacin rai. Sau da yawa abin da yake fushin ko rigima akai zaka ga babu wani dalilin yi hakan.

8- Rashin iya saduwa da matansa. Ana yin gane an yi wa mutum sihiri ta hayar mutum ya kasa saduwa da iyalinsa alhali mazakutansa lafiya kalau ta ke.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *