ALAMOMIN CIWON HANTA

Ciwon Hanta na nufin cutar kumburin hanta wanda ta ke faruwa sanadiyar ƙwayoyin cuta masu yaɗuwa, harwayau tana faruwa sanadiyar shan giya, shan magunguna ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma ta sanadiyar yawan sinadiran dake cikin magunguna.

NAU’O’IN CUTAR HANTA

Akwai manyan nau’in cutar Hanta kamar haka:
1- Hepatitis A : Wannan nau’in ciwon Hanta na faruwa ne ta sanadiyar ƙwayar cutar (HAV) idan hanta ta kamu da irin wannan cutar wani lokaci a kan warke cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

2- Hepatitis B : Wannan nau’in ciwon hanta ya fi haɗari dan haka yana da muhimmanci idan an kamu da shi a ɗauki matakan da suka dace wajen ta hanyar tuntubar ƙwarraru da kuma shan magungunan da suka dace domin rabuwa da wannan cuta. Hukumar (CDC) ta ce sama da mutane miliyan 257 ke ɗauke da cutar hepatitis B.
3- Hepatitis C
4 – Hepatitis D

5- Hepatitis E : Ita wannan cutar ana kamuwa da ita ta hanyar shan ruwa mai ɗauke da wannan ƙwayar cutar ke nan anfi kamuwa da ita a wuraren da akwai karancin tsaftace mahalli.

ALAMOMIN CIWON HANTA
1- Yawan kasala da raunin jiki
2- Yawan ciwon kai
3- Tashin Zuciya
4- Canzawa launin fata zuwa kore haka ma idon mai ɗauke da wannan cutar ka iya canzawa zuwa kore.
5- Rama: Mutumin dake dauke da ciwon hanta ka iya fuskantar matsalar rama
6- Rashin son cin abinci
7- Ciwon gaɓoɓi
8- Yawan zazzaɓi
9- Duhun fitsari

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *