SIHIRIN RUFA’IDO/DAUKAR IDO KO DABO:

Sihirin daukar ido ko rufa’ido yana daga cikin sihirin mutanen Fir’auna wanda Al-Kur’ani mai girma ya zo da kisarsa. Aya ta 66 a cikin suratul Daha ya yi bayanin yadda wannan nau’in sihirin yake. Ga ayar kamar haka:

قَالَ بَلۡ أَلۡقُواْۖ فَإِذَا حِبَالُهُمۡ وَعِصِيُّهُمۡ يُخَيَّلُ إِلَيۡهِ مِن سِحۡرِهِمۡ أَنَّهَا تَسۡعَىٰ 

Fasara:

Suratul-Daha 66. Ya ce, ‘A’a, ku fara jefawa. Sai ga igiyoyinsu da sandunansu, suna daukar idonsa, kamar suna tafiya, don sihirinsu.’

Su masu sihirin Fir’auna sun zo da igiyoyi da sanduna sukayi abubuwansu na sihiri sai ga sandunan da suka zo da su sun zama macizai sai ka ga igaya na tafiya duk wannan rufa ido ne amma a hakika ba haka abin yake ba. Daga cikin abubuwan da masu wannan nau’in sihiri suke yi sun hada; mai sihirin na iya daga hularsa sai kaga wuta na ci a kansa da hularsa din, ko ya tura wani karfe mai tsini da tsayi cikin hancinsa, ko ya shigar da rakumi cikin bakinsa, ko kaga gemunsa na kamawa da wuta wani lokaci sukan rufe kwano babu komai amma idan suka bude sai kaga kayayyaki ko kudade.Wadannan dukkan sihiri ne na dabo ko kuma rufa ido domin ainin abin da ka ke gani suna yi ba haka bane a hakika.

Abu- Hanifa Rahimahullah ya raba sihiri zuwa nau’i biyu: Sihiri na gaskiya (na hakika) da kuma sihirin rufa ido. Sihirin rufa ido a ido ne kawai ka ke ganin abin amma ba gaskiya ba ne, amma sihiri na hakika shi yana faruwa ne a hakikani misali: Sihiri na hakika yana iya tasirantuwa a jikin mutum yana iya sanya wa mutum rashin lafiya ko kuma ya zama dalilin ajalinsa ko a raba mutum da matarsa. Amma sihirin rufa ido ba shi da wannan irin tisirin.

ALAMOMIN SIHIRIN RUFA IDO:

Daga cikin alamomin da ake gane sihirin rufa ido ko daukan ido sun hada:

1- Mutum zai ga abin da yake tabbace a gurin guda yana motsi ko kuma abu mai motsi ya gansa tabbace waje guda baya motsi.

2- Za a ga abu karami babba ko kuma a ga abu babba karami

3- Mutum zai rinka ganin abubuwa ba yadda suke ba a hakika kamar mutum ya ga igiya ya koma maciji yana tafiya.

YADDA AKE BATA SIHIRIN RUFA IDO:

Ana lalata wannan nau’in sihirin da duk wani abu da yake korar shaidanu. Misali:

1- Ana yin kirar sallah

2- Ana karanta ayatul-kursiyyu tana da matukar tasiri wanje warware wannan sihiri.

3- Azkar na shari’a wadanda suke kuran shaidanu.

4- Yawaita karanta Bismillahi Rahmani Rahiim

Da sharadin mutum ya kasance cikin alwala idan aka yi haka sihirin bai lalace ba to a dauki wani mataki tayiwu ba mai sihiri ba ne.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *