SIHIRIN HANA MACE AURE

Manufar wannan nau’in sihirin shi ne hana Mace aure ta hanyar tura mata aljani ko aljanu da za su sanya ta ta ji bata son duk wani namiji da ya zo nemanta da aure ko kuma su mazajen sun rinka ganinta da mummunar kama ta yadda ba za su so ta da aure ba.

YADDA AKE KULLA SIHIRIN HANA MACE AURE:

Mutum mugu makiri zai je wajen mugun Boka ya nemi ya yi masa sihirin da zai hana diyar wani aure, shi wannan mai sihirin zai nemi ya fada masa sunanta da na mahaifiyarta da kuma wani abu nata kamar gashin kai, suturanta da sauransu. Sai ya fara hada masa sihirin ta hanyar tura mata aljani daya ko fiye da haka,wanda zai rinka bibiyar wannan budurwar/bazawarar har sai ya shiga cikin jikinta sai sanya ta rinka jin wadannan yanayin da za mu kawo kamar haka:

1- Tsoro mai tsanani

2- Yawan mantuwa da gafala

3- Yawan sha’awar jima’i (hakan na iya jefa ta cikin zinace-zinace)

4- Saurin fushi

Wannan aljanin/aljanu zai sanya mata halaiya da za su kasance kamar haka:

1- Kodai ya shiga cikin jikinta ya rinka sanyawa jin kunci ga duk namijin da ya zo nemanta da aure har sai ta kore shi zata samu sauki.

2- Ko kuma idan bai samu damar shiga jikinta ba sai ya tsaya daga waje ya na canza mata kamanni ta yadda duk namijin da ya zo nemanta ya rinka ganinta da mummunar kama sai ya jefa mashi waswasi akanta. Sai ka ga duk wanda ya zo nemanta ba zai sake dawowa ba ko da kuwa da farko sun aminta da juna. Idan sihirin yayi tasiri sosai zai kasance duk namijin ya je kofar gidansu zance, tun daga kofar gida zai shiga cikin yanayin kunci mai tsanani tare da damuwa zai ji shi kamar wanda aka sanya a kurkuku dan haka ba zai sake dawowa ba.

ALAMOMIN SIHIRIN HANA MACE AURE:

Ana iya fahimtar an yi wa mace sihirin hana aure ta hanyar wadannan alamomin da za mu kawo kamar haka:

1- Ciwon kai nan da can ta yadda ko da ta sha maganin ciwon kai ba za ta samu sauki ba.

2- Zata rinka jin kunci mai tsanani a kirjinta, musamman daga bayan la’asar zuwa tsakiyan dare.

3- Yawan tunani wani lokacin har a fita hayyaci.

4- Yawan shiga damuwa a tsakiyar bacci/kwana

5- Wani lokaci zai kasance a koda yaushe tana jin zafi a cikinta.

6- Ciwon baya daga kasa.

HANYOYIN MAGANIN SIHIRIN HANA MACE AURE:

A kan yi wa matar da aka yi wa sihirin hana mace aure rukiya idan aljanin yayi Magana sai a nemi ya fita daga jikinta a nan take. Idan kuma ba a ji alamar bayyanarsa ba sai a bata shawarar daukan matakai kamar haka:

1- Ta rinka kiyaye sallah tare da yin sallar a cikin lokaci.

2- Ta rinka kwantawa bacci da al’awala kuma ta rinka karanta ayatul-kursiyu idan za ta kwanta bacci.

3- Hada tafin hannu a lokacin bacci sai a karanta suratul falaq da suratul Nasi a tufa a shafe jiki sau uku.

4- kullum a saurare sautin karatun ayatul kursiyu da aka sajjala sau uku.

5- A rinka karanta ayoyin rukiya wanda muka kawo a baya a cikin ruwa mai tsafta da tsarki ana sha ana wanka na tsawon kwana uku a jere.

6- Ta rinka zikirin “La’ilaha illah wahdahu lasharikalahu lahul-mulku wa lahul-hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadir”. لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد، وهو على كل شيء قدير،

Kafa 100 bayan sallar asuba.

7- Ana son mai fama da wannan matsalar na sihirin hana aure ta daina sauraren kide-kide da waqe-waqe kuma har wayau ta yi ta maimata magagungunan da muka kawo a kalla na wata guda da yardan Allah sihirin zai lalace.

Click here to go to our website: www.alwahada.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *