SIHIRIN SOYAYYA
Sihirin soyayya shi ne duk wani aiki na sihiri Wanda ake so a kusantar da mutum da son wani, kamar kusantar da miji ya so matarsa ko mata ta so mijinta ko budurwa ta so wani saurayi, wannan kuma sananne ne a cikin mutane. Kamar yadda ake kiranshi da sihirin soyayya ko mallaka kuma masu sihirin sukan kira shi da sihiri kawo masoyi, kishiyar wannan nau’in sihirin shi ne sihirin rabuwa,kuma ana amfani da al’ajanu da shaidanu waje aiwatar da wadannan nau’o’in sihirin.
Yadda ake hada sihirin soyayya:
Wanda yake so a yi masa sihirin soyayya ko hada kauna tsakaninsa da wani yakan je wajen mai sihiri ko Boka ya fada masa yana son a kulla masa soyayya da wani ko wata daga nan mai sihirin zai nemi sunan mutumin da yake so ayi wa sihirin da sunar mahaifiyarsa, kamar yadda zai iya bukatar da a zo masa da kasar tafin kafafunsa, gashinsa, kumbarsa (farcensa) ko hotonsa. Hakika mai sihirin zai iya neman wani nau’i na turare da zai kulla wannan sihirin.
Wuraren da ake sanya sihirin soyayya:
Akwai wurare da dama da suke sanya wannan sihiri amma wadanda suka fi shahara sun hada da:
1- Su kan sanya wannan sihirin a cikin abinci ko abin sha ko kudi ko kuma wani kyauta da za su ba wanda ake so ayi wa sihirin.
2- Su kan sanya wannan sihirin a jikin fatar dabba ko kuma su ba kare/karya ta ci wanda hakan zai sanya wanda aka yi wa sihirin ba zai iya rabuwa da su ba komai wulakanci da za su masa.
3- Wani lokaci sukan watsa sihirin a suturar mutumin da suke son suyi wa sihiri ko a kan hanyar da ya ke bi ko a cikin dankin da yake kwana.
4- Sukan daure/kulla sihirin a jikin itaciya ko in da iska zai rinka kada shi.
5-Wani lokaci masu sihirin sukan kulla sihirin a jikin tsuntsu.
ALAMOMIN SIHIRIN SOYAYYA
Akwai alamomi masu yawa da suke bayyana ga wanda aka yi wa sihirin soyayya wanda suka hada da:
1- Tsananin kauna da soyayyar da ta zarce al’ada. Misali: Labarin wani mutumin da aka yi wannnan nau’i na sihirin hakan ya sanya duk inda yake yana tunanin matarsa idan ya dawo gida baya samun kwanciyar hankali sai ya ganta idan tana wajen girki sai ya bita wajen duk inda ta bi. Hakan ya jefa su cikin matsala ba dan kadan ba.
2- Daga cikin alamomin sihirin soyayya shi ne Wanda aka yi wa wannnan sihirin zai kasance mai yawan son jima’i.
3- Biyayya ga wanda ya yi masa sihirin ido rufe. Wato zai kasance duk abin da wanda ya yi masa sihirin ya ce ya yi zai yi ne kawai ba tare da la’akari da munin abun ba ko da kuwa sabon Allah ne.
4- Ba zai so ya rabu da hoton wanda ya yi masa sihirin ba, kuma a koda yaushi zai rinka ji tsananin son ganinshi/ta. Idan kuma suka hadu zai firjita ya tsorata tare da ganin kwarjinsa ba tare da wani dalili na hankali ba.
5- Yawan ciwon kai kuma ko ya sha magani ba zai warke ba.
Dalilan da ke sa ayi Sihirin Soyayya
1- Idan ana yawan samun sabani a tsakanin ma’aurata.
2- Idan Mace tana son ta mallaki dukiyar mijinta musamman idan madawaci ne.
3- Idan ya kasance Mace na tsoron mijinta ya yi mata kishiya. Mata masu tsananin kishi wadanda ba sa son mijinsu ya kara aure hakan kan jefa su su aikata sihirin soyayya idan na karancin tsoron Allah
Illolin dake tattare da sihirin Soyayya
1- Wani lokaci Wanda aka yi wa sihirin yakan kamu da rashin lafiya akwai mutumin da ya yi ta fama da rashin lafiya kusan shekaru uku a sanadiyar wannan sihirin.
2- Wani lokaci a Kan samu akasin haka maimakon soyayya sai ya zama kiyayya wannan na faruwa saboda jahilcin masu sihirin da kuma kura-kure da ake yi wani lokaci waje aikata sihirin.
3- Wani lokaci Mace kan yi wa mijinta sihirin da zai kasance baya son kowace Mace sai ita kadai, hakan yana sabbaba mijin ya ji yana tsananin kin mahaifiyarsa, goggoninsa kanansa mata da yayyinsa da dukkanin danginsa mata.
4- Wani lokaci idan Mace ta yi wannan nau’in sihirin na soyayya wanda mijin zai ki duk wata mace sai ita kadai.Hakan kan sanya har itama din mijin ya kasance baya sonta. Wata ta yi irin wannan nau’in sihirin sai ya kasance abin ya juya mijin ya zo baya kaunarta kwata-kwata har ya kai ga ya saketa ko da ta koma wajen bokar ta tarar da ya mutu.
Yadda ake warware sihirin rabuwa:
Ana iya lalata sihirin soyayya ta wadannan hanyoyi kamar haka:
1- Ana iya yi wa wanda aka yi sihirin soyayya rukiya ta shari’a. A baya mun kawo bayanin ayoyin rukiya ana iya karanta wa mai wannan sihirin sau uku a rana ko ya rinka sauraren sautin karatunsu sau uku a rana amma da sharadi yayi niyyar neman waraka a wajen Allah kuma ya kasance cikin alwala.
2- Ana iya yi masa hijama (kaho) shi ma yana lalata nau’o’in sihiri da dama.
3- Amfani da kusdul-Hind: Wanda aka yi wa sihirin soyayya yana iya shan garin kusdul-hind cikin ruwan zafi da zuma da safe da yamma sannan zai rinka safa man kusdul-hind da safe da yama. Har ila yau ana son wanda aka yi wa sihirin soyayya ya rinka hayaki da garin kusdul-hindu.