DALILAI DAKE NUNI DA SAMUWAN SIHIRI

Akwai dalilai masu yawa daga cikin ayoyin Al-Kur’ani mai girma da ke nuni da samuwar sihiri. Ga wasu kadan daga cikin ayoyin Al-Kur’ani da suka tabbar da cewa akwai sihiri kuma ana aikata shi:

 

وَاتَّبَعُوا مَا تَتْلُو الشَّيَاطِينُ عَلَىٰ مُلْكِ سُلَيْمَانَ ۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَٰكِنَّ الشَّيَاطِينَ كَفَرُوا يُعَلِّمُونَ النَّاسَ السِّحْرَ وَمَا أُنْزِلَ عَلَى الْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَارُوتَ وَمَارُوتَ ۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ ۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَيْنَ الْمَرْءِ وَزَوْجِهِ ۚ وَمَا هُمْ بِضَارِّينَ بِهِ مِنْ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنْفَعُهُمْ ۚ وَلَقَدْ عَلِمُوا لَمَنِ اشْتَرَاهُ مَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ خَلَاقٍ ۚ وَلَبِئْسَ مَا شَرَوْا بِهِ أَنْفُسَهُمْ ۚ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ. (سورة البقرة ١.٢)

FASSARA:

Kuma sun bi abin da shaiɗanu ke bi don karya mulkin Sulaiman. Sulaiman bai kafirta ba, amma Shaiɗanu ne suka kafirta. Sona koya wa mutane sihiri. Kuma suna riya bin abin da aka saukar wa Mala’iku biyu, a Babila – Haruta da Maruta. Su kuwa ba sa koya wa kowa komai, sai sun ce. Haƙiƙa, mu fitina ne, kada ka kafirta. Daga gurinsu su ke koyon abin da suke amfani da shi, suke rarraba tsakanin mutum da matarsa, kuma ba su cuci kowa da shi ba, sai da yardar Allah. Kuma (masu hamayya da Annabi), suna koyon abin da zai cuce su ne, ba zai amfane su ba. Kuma suna sane cewa, wanda ya yi mu’amala da shi, ba shi da rabo a Lahira. Kuma abin da suka sayar da kansu da shi, ya munana idan sun sani.

 

Har wayau, Allah ya ba mu labari dangane da abin da ya auku a tsakanin Annabi Musa (A.S) da masu Sihirin Fir’auna ya gayyata. Ga abin da Allah yak e cewa:

 

فَلَمَّا أَلْقَوْا قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئْتُمْ بِهِ السِّحْرُ ۖ إِنَّ اللَّهَ سَيُبْطِلُهُ ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ (سورة يونس ٨١)

وَيُحِقُّ اللَّهُ الْحَقَّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ (سورة يونس ٨٢)

FASSARA:

  1. Yayin da suka jefa, Musa ya ce, ‘Abin da da kuka zo da shi Sihiri ne kawai. Allah kuwa zai ɓata shi, haƙiƙa, Allah ba ya gyara aikin maɓarnata.’
  2. Kuma Allah yana tabbatar da gaskiya ta kalmominSa, ko masu laifi basa so.

Ayoyin da suka yi Magana akan sihiri suna da yawa ga duk wanda ya yi san addinin Musulunci zai fahimci hakan.

DALILAI NA SUNNA AKAN SAMUWAR SIHIRI:

Akwai hadisai da dama da aka ruwaito wanda ke nuni akan samuwan sihiri da kuma haramcinsa amma za mu takaitu da daya daga ciki. Ga Hadisin kamar haka:

قال الرسول صلّى الله عليه وسلّم: (ليس منَّا من تَطيرَ أو تُطيرَ له، أو تَكهَّن أو تُكهِّنَ له، أو سَحر أو سُحر له، ومن أتى كاهناً فصدَّقَه بما يقولُ فقد كفر بما أنزل على محمدٍ صلَّى اللهُ عليهِ وسلَّمَ

FASSARA:

Manzon Allah Tsira da Amincin Allah da iyalan gidansa ya ce: “Baya tare da mu duk wanda ya yi canfi ko ya je aka yi masa canfi, ko ya yi duba ko ya je aka yi masa, ko yayi sihiri ka ya je aka yi masa, wanda ya je wajen Boka kuma ya yarda da abin da ya ke cewa to hakika ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (Sallahu alaihi wa alihi wasallam)’’.

TAMBIHI: Larabawa a lokacin jihiliya sun kasance suna canfi misali idan mutum zai yi tafiya sai ya saki tsuntsu idan tsuntsun ta tashi ta bi bangaren dama zai ya ci gaba da tafiyarsa idan ta tashi ta bi ta bangaren hagu sai ya canfa tafiyar ya dawo gida, ya fasa ba zai yi tafiyar ba. Sannan akwai masu da’awar sanin gaibu ko kuma su je wajen bokaye ayi masu duba tare da bincike akan abin da zai faru da su anan gaba.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *